A kauracewa abinda zai karya demokaradiya – Janar Abdussalami

Kwamitin sasanta ‘yan takarar shugabancin kasar nan da tsohon shugaban mulkin soji Janar Abdussalami Abubakar mai ritaya ke jagoranta; ya bukaci al’ummar Najeriya da su guji aikata wani abu da ka iya janyo nakasu ga dorewar mulkin dimukuradiyar kasar nan.

Kwamitin ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su mai da batun dage zabukan kasa da hukumar zabe kasa ta INEC ta yi a matsayin wani mataki da ya zama dole, a don haka ya bukace su da su kasance masu kishin kasa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin Janar Abdussalami Abubakar da mai masaukin taron kwamitin Bishop Mathew Hassan Kukah.

A cewar sanawar, kwamitin yana sane da cewa al’ummar kasar nan ba su ji dadin halin da suka tsinci kansu ba sakamakon sauya lokacin gudanar da zaben, sai dai sun ce yana da kyau al’ummar Najeriya su dauki lamarin a matsayin kaddara.

Ta cikin sanarwar da kwamitin ya fitar dai ya kuma ce kamata ya yi al’ummar kasar nan su rika tunanin gaba maimakon waiwayen abinda ya faru a baya domin daukan darasi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *