AITOE CUP 2018: Rangers FC ta doke Kano Pillars a bugun fenariti

Kungiyar Kwallon Kafa ta Rangers dake Najeriya ta nuna bajinta a karawarsu da Kano Pillars a gasar cin kofin kalubale wato Aiteo Cup, bajintar da ta baiwa yan kallo mamaki.

Rangers wadda ta lashe kofin gasar, ta rama dukkanin kwallaye 3 da Kano Pillars ta fara zura mata, abin da ya sa a kai ga bugun fanariti har kuma ta samu nasarar daga kofin na bana.

Rabiu Ali da Jimoh Isma’ila na Pillars dukkaninsu sun barar da bugun fanaritinsu, yayin da ‘yan wasan Rangers hudu suka zura nasu fanaritin, abin da ya sa aka tashi wasan 4-2.

An dai gudanar da wasan ne a filin wasa na Stephen Keshi da ke daukar mutane dubu 25 a birnin Asaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *