Al’umma a kauyen Zamfara sun afkawa ‘Yan bindiga

Al’ummar garin kauyen Dan Jibga da ke yankin karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, sun kashe ‘yan bindiga hamsin da tara wadanda suka kawo hari kauyen nasu.

Haka zalika bakwai daga cikin al’ummar kauyen sun rasa rayukansu sakamakon batakashin da ya dau tsawon a wanni hudu ana fafatawa.

Rahotanni sun ce a Talatar nan ne ‘yan bindigar wadanda yawansu ya kai dari da tamanin suka isa kauyen na Dan Jibga dauke da manyan makamai lamarin da ya sa al’ummar kauyen wadanda ke cikin shirin kota kwana suka debo makamai domin kare kansu wanda a sanadiyar hakan suka kashe ‘yan bindigar hamsin da tara.

Wasu shaidun gani da ido sun ce tuni kwambar motocin sojoji suka isa kauyen sannan suka kafa sansani domin shirin tunkarar ko da ‘yan bindigar da suka tsira da rayukansu ka iya dawowa domin daukar fansa.

Mukaddashin mai magana da yawun rundunar sojin kasar nan manjo Clement Abiade, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce, tuni sojoji suka bazama a dazukan da ke yankin domin gano ‘yan bindigar da suka tsere da raunuka a jikinsu.

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *