An nada sabbin kwamandojin yaki da Boko Haram a Najeriya

Babban hafsan tsaron Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai ya nada sabbin manyan kwamandoji da ke bada umarnin ga rundunonin hukumar na musamman wadanda ke yaki da mayakan Boko Haram.

Wannan nadin dai ya biyo bayan umarnin da Ministan tsaron kasar nan Mansur Dan-Ali ya bayar, na cewa a sauya fasalin rundunar Operation Lafiya Dole don samun cikakkiyar nasarar da ake bukata a yakin da suke yi a yankin arewa maso gabashin kasar nan.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labaran Rundunar Brigediya Janar Sani Usman ya fitar ta bayyana cewa an yi hakan ne don shigo da sabbin jini cikin al’amarin tabbatar da tsaro a kasar, inda kuma yace cikin gyaran da aka yi ya hadar da sauyin guraren aiki ga manyan jami’an hukumar da kuma Karin girma ga wasu.

Cikin wadanda aka yiwa Karin girman akwai OT Akinjobi wanda shine shugaban sashin da ke sanya ido na rundunar, wanda aka karawa girma zuwa kwamandan sashi na uku na rundunar Operation Lafiya Dole da sauran su.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *