An raba kudaden arzikin kasa a Najeriya

Gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi a Najeriya sun raba naira biliyan dari shida da goma da miliyan dari hudu a matsayin kasonsu na arzikin kasa a watan Fabrairu.

Akanta Janar na kasa Ahmed Idris ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai jiya a Abuja bayan kammala taron kwamitin rabon arzikin kasa.

A cikin wata takardar bayan taro da ofishin akanta Janar na kasa ya fitar ta bayyana cewa, tsuran kudaden harajin da aka tattara a watan Janairu ya gaza na watan Disamban bara.

Sanarwar ta kuma ce a watan na Janiaru an tattara naira biliyan dari biyar da biyar da miliyan dari biyu da arba’in da shida, yayin da a watan Disambar shekarar da ta gabata aka tara naira biliyan dari biyar da arba’in da bakwai da miliyan dari hudu da sittin da biyu.

A cewar sanarwar, gwamnatin tarayya ta samu sama da naira biliyan dari biyu da hamsin da biyu da miliyan dari hudu da goma sha biyu, yayin da jihohi talatin da shida na kasar nan suka karbi naira biliyan dari da saba’in da miliyan dari biyar da arba’in da daya sai kuma kananan hukumomin da suka karbi jimillan naira biliyan dari da ashirin da bakwai da miliyan dari tara da ashirin da uku.

Haka zalika suma jihohi da ke da arzikin man fetur sun karbi nasu kaso goma sha ukun wanda ya kai naira biliyan goma sha bakwai da miliyan dari biyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *