An rantsar da mai shari’a Uwani a matsayin shugabar kotun kolin Najeriya

Babban jojin Najeriya mai shari’a walter Onnoghen ya rantsar da mai shari’a Uwani Musa Abba Aji a matsayin shugabar kotun kolin kasar bayan da ta shafe shekaru 14 tana jagorantar kotun daukaka kara.

An dai rantsar da ita ne a kotun kolin da ke babban birnin tarayya Abuja. A yayin bikin rantsuwar dai babban jojin kasar nan ya yi kira gareta da ta yi aiki tukuru cikin gaskiya da rikon amana don ciyar da harkokin shari’a gaba a kasar nan.

Ya kuma kara da cewa ranstuwar tata na zuwa ne a dai-dai lokacin da kotun kolin ta cika da shari’o’I a don haka ya kamata ta zage damtse.

Daga nan kuma sai ya yi kira ga kafatanin alkalan kasar nan da su rike gaskiya a yayin gudanar da aikin su yadda ya kamata, inda yace ya zama dole ko wane alkali ya zo aiki cikin shirin fuskantar kowane irin kalubale.

 

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *