‘Yan bindiga sun sace tare da yin garkuwa da mai dakin shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Nassarawa Suleiman Abubakar, Yahanasu Abubakar.

Suleiman Abubakar ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe bakwai na yammacin jiya akan titin Gudi-Garaku da ke yankin karamar hukumar Akwanga a jihar ta Nassarawa.

A cewar sa ‘yan bindigar sun yi harbi a motar safa mallakin kungiyar ‘yan jaridu ta kasa wanda matar sa ke ciki bayan sun baro garin Keffi, inda taje ta yi rajista a sansanin ‘yan hidimar kasa.

Da ya ke mai da jawabi kan faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Nassarawa Sama’ila Usman, ya ce tuni suka baza jami’ansu don ceto matan da aka sace

Haka zalika ‘yan bindigar sun kuma sace matar wani tsohon dan majalaisar jihar ta Nassarawa wadda ta ke cikin motar ta su da kuma wasu mata biyu da ke wata motar ta daban.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *