Bangarorin gwamnatin Najeriya uku ne da suka hadar da gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma kananan hukumomi suka amfana da rabon tattalin arzikin kasa na watan da ya gabata da yakai naira biliyan dari shida da sha tara da dari takwas da hamsin da bakwai.

Sai dai kwamitin y ace kudin yayi kasa da da kudaden da aka tara a watannin baya da ya kai naira biliyan dari biyar da biyar da kuma miliyan dari biyu da arba’in da shida.

Cikin takardar bayan taro da kwamtin rabon tattalin arzikin kasar ya fitar ya ce cikin watan fabrairu kasar nan ta tara harajin naira biliyan dari hudu da saba’in da takwas da miliyan dari hudu da talatin da hudu.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala zaman kwamitin na jiya daraktan da ke kula da hada-hadar kudi a ofishin akanta janar na kasa Muhammad Usman ya ce bangaren mai ya kawo dala milyan 557

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *