Atletico Madrid ta doke Najeriya a wasan sada zumunci

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta Spaniya ta doke Najeriya da ci 3-2 a wani wasan sada zumunta da suka buga a kasar ranar Talata.

‘Yan wasan Super Eagles ne suka fara zura kwallo a ragar Atletico Madrid a minti na 32 da fara wasan, kafin Angel Correa ya farke kwallon a minti na 33.

Wasan ya koma 2-1 ne a minti na 64, bayan da Fernando Torres ya zura kwallo a ragar Najeriya. Sai dai an farke kwallon a minti 80, inda wasan ya koma 2-2.

Amma kuma Atletico Madrid ta kara zuwa Najeriya kwallo a raga ana saura minti 10 a tashi wasan.

An yi wasan sada zumuntar ne a wani bangare na shirye-shiryen da kasar ke yi domin tunkurar gasar cin kofin duniya, wadda za a fara a watan gobe a kasar Rasha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *