Burtaniya ta gamsu da zaben shugaban kasa a Najeriya

Kasar Burtaniya ta ce ta gamsu da sakamakon zabukan shugaban kasa dana ‘yan majalisun dokokin Najeriya  da aka gudanar a kasar ranar Asabar da ta gabata.

Minista mai kula da nahiyar Afirka Harriett Baldwin ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

A cewar sanarwar, zaben da sakamakon sa an yi sune akan idanun masu sanya idanu na cikin gida da a ketare, wanda kuma dukkanninsu sun yaba da sakamakon sa.

Harriett Baldwin a cikin sanarwar ya kuma taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari Murnar sake darewa karagar mulki karo na biyu.

Haka kuma sanarwar ta kuma ce al’ummar Nigeriya sun nuna irin bajinta da kuma wayewa da suke da shi a bangaren dimukuradiya ,a don haka ta bukaci hukumar zabe ta kasa INEC da ta yi gyara a dan bangarorin da aka samu matsaloli a yayin zaben na makon jiya a zabukan da za a yi anan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *