CBN a Najeriya ya bankuna wa’adin shekaru biyar

Babban bankin Najeriya CBN ya sanya wa’adin shekaru biyar ga dukkanin bankunan kasar kafin su lalata dukkanin wani cakin kudi da abokan huldar su suka gabatar musu domin karbar kudi.

Wannan na kunshe cikin wata sabuwar dokar tantance lamuran kudi da babban bankin ya fitar, a cewar bankin wannan sabon tsari zai taimaka wajen samar da nagartaccen aikin banki a kasar.

Wannan doka dai ta yi dai-dai da tsarin dokokin da ikon da doka ta baiwa babban bankin kasar a sashi na 2 (d) da na 33 (1) (b) na shekarar 2007 domin inganta harkokin kudi a kasar.

Wannan sabuwar doka da babban bankin kasar ya fito da ita wacce ta fara aiki nan take, ya ce dukkanin bankin da ke da lasisi, kuma baya cikin wannan tsari to lallai ya shiga domin bin wannan doka ta adana chakin kudin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *