Dalibai sama da 800,000 ne sukayi rijistar JAMB a Najeriya

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da Sakandire ta Najeriya (JAMB) ta ce dalibai dubu dari takwas da sittin da tara da dari bakwai da tara ne suka yi rajista domin rubuta jarabawar wannan shekara da za a yi a watan Maris 2019.

Hakan na kunshe ne cikin rahoton da hukumar ke fitarwa a mujallarta na mako-mako.

Hukumar ta JAMB ta kuma ce ta soke wasu cibiyoyin rubuta jarrabawar guda tara sakamak on karya ka’idoji da su ka yi.

Rahoton na hukumar JAMB ya kara da cewa, cibiyoyin da aka soke lasisin su, sun bukaci kudade fiye da adadin da gwamnati ta ayyana.

Haka kuma hukumar JAMB ta ce ana ci gaba da binciken wasu cibiyoyi guda goma da ke jihohin Lagos da Filato.

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *