Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), ta ce, za ta rika aiki tare da hukumar kula da masu yiwa kasa hidima (NYSC) wajen dakile ayyukan batagari.

Hukumar ta EFCC ta ce ta karbi korafe-korafe daga hukumar masu yiwa kasa hidima (NYSC), cewa, akwai wasu marasa kishin kasa da suke sayar da takardar shaidar kammala karatun su ga wadanda basu kammala karatu ba wajen gudanar da hidimar kasa.

Mai rikon mukamin shugaban hukumar ta (EFCC), Ibrahim Magu ne ya bayyana haka jiya a birnin tarayya Abuja yayin zantawa da darakta Janar na hukumar masu yiwa kasa hidima Brigadier Janar Shuaibu wanda ya kai masa ziyara ofishin sa.

Anashi bangaren shugaban hukumar masu yiwa kasa hidima brigadier Janar Shu’aibu cewa yayi za su yi duk me yiwuwa wajen ganin an dakile ayyukan batagari.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *