Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce tana binciken gwamnan jihar Imo mai barin gado Rochas Okorocha da kuma wasu manya kusoshin gwamnatin Najeriya bisa zargin su da almundahana da dukiyoyin al’umma.

Shugaban hukumar ta EFCC Ibrahim Magu ne ya bayyana haka, cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a birinin Landon.

Magu ya kara da cewa, ya kai ziyara Burtaniya ne domin ganawa da masu ruwa da tsaki wajen binciken laifukan da suka danganci cin hanci da rashawa da kuma wasu manya laifuka.

A cewar sa, hukumar ba ta kai matakin binciken da zata bayyana wa jama’a halin da ake ciki ba akan binciken da ta keyi wa gwamnan jihar ta Imo da wasu manya jami’an Gwamnatin.

Magu ya kina ce daga cikin tuhumar da hukumar ke yiwa gwamna Rochas Okorocha, akwai Zargin yin al’mundahana da kudaden Paris Club da aka dawo wa jihohin kasar da su, don biyan Albashin ma’aikata da adadin su ya kai Naira Biliyan 8.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *