Farfesa Osinbajo na halartar taron shugabanin Afrika

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya na kasar Austria don halattar babban taron shugabanin Afrika da na tarayyar Turai da ake yi Vienna ta kasar Austria.

Mai Magana da yawon Mataimakin shugaban kasar kan kafafan yada labarai Laolu Akande ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fita a yau a Abuja cewa gwamnatin kasar Austria ce ta shirya karbar  bakwancin taron a madadin tarayya Turai da kungiyar tarayyar Afrika.

A cewar sanarwar farfesa Osinabjo zai gabatar da jawabi mai taken ‘’’Goyan baya wajen amfani da cigaban zamani’’ wanda za’a fara daga yau Litinin 17 zuwa gobe Talata 18 ga wannan wata A cewar wanda suka shirya taron na EU da AU, taron zai sanya a fitar da sababin tsare-tsare wajen yin amfani da sababbin kirkiri kasancewar ana cikin amfani da internet don cigaban zamani da bunkasa ayyuka, ta yadda kowa da kowa zai amfana daga sauyin da Internet ya zo da shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *