Gwamnati da ‘Yan Kwadago suna cigaba da tattaunawa a Najeriya

Kungiyar kwadago zata ci gaba da ganawa da gwamnantin tarayyar Najeriya kan batun mafi karancin albashi bayan ganawar da suka yi a ranar juma’ar da ta gabata, wanda aka tashi taron ba tare da an cimma wata matsaya ba.

Kungiyar kwadagon dai na bukatar gwamnatin kasar ta mika kudurin dokar mafi karancin albashi gaban majalisun tarayyar kasar nan don mayar da shi doka.

Jim kadan bayan kammala taron da kungiyar ta kudanar da gwamnantin tarayya a ranar juma’ar da ta gabata shugaban kungiyar na kasa Ayuba Wabba ya shaida cewa kungiyar zata kuma zama da gwamnantin tarayya a yau litinin.

Ya kuma kara da cewa zasu yi ganawar ta yau ne da misalin karfe 5 na yamma, inda yace badon shirin tattaunawar ba, kungiyar ta shirya tsunduma yajin aiki a Litinin din nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *