Hada kai da Sarakuna zai taimaka wajen inganta ilimi – Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya bukaci masu rike da sarautun gargajiya da su yi aiki kafada-da-kafada da hukumar bada ilimin manya da nufin samun ingantaccen ilimi a yankunansu.

Sarki Muhammadu Sanusi II na wannan umarnin ne a yayin da jami’an hukumar kula da ilimin manya ta jiha a karkashin jagoranci babban Darakta, Abdulmumin Liman Yusuf, suka kai masa ziyara a fadar sa.

Sarkin ya bayyana cewa akwai bukatar hukumomin ilimi su farfado da rubutun karatun ajami da nufin inganta ilimin ajamiwanda magabata sukai amfani dashi tun farko wajan cimma burinsu na rayuwa kafin shigowar ilimin nasara a kasashen Hausa.

Tun farko da yake jawabi, Babban daraktan Hukumar Abdulmumin Liman yace sun zo fada ne da nufin sanarwa da sarki irin ayyukan hukumar nailimantarwa da fadakarwa akan muhimmancin ilimi.

 

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *