Jam’iyyun Adawa a Sokoto sunki amincewa da nasarar Tambuwal

Gamayyar jam’iyyun adawa guda ashirin da takwas sun ki amincewa da nasarar da gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya samu na zarcewa a karo na biyu a yayin zaben gwamnan jihar da aka gudanar a baya-bayan nan.

Jam’iyyun sun bayyana matsayar ta su ce yayin wani taron manema labarai jiya a garin Sokoto.

Da ya ke jawabi a madadin sauran jam ‘iyyun, dan takarar gwamna a tutar jam’iyyar NEPP, Musa Aliyu, ya ce, gamayyar jam’iyyun baki daya ba su gamsu da sahihancin sakamakon zaben ba.

Ya ce a yayin zaben an tabka magudi da cin zarafin masu kada kuri’a wanda hakan ya sabawa dokokin zabe dama kundin tsarin mulkin kasar nan.

adi da ta gabata ne hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana Aminu Waziri Tambuwal na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya samu nasara a zaben gwamnan na jihar Sokoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *