Majalisar dinkin duniya ta ce kaso biyu cikin uku na mutanen da su ka yi fama da matsanancin yunwa a shekarar da ta gabata sun fito ne daga wasu kasashe takwas ciki har da Najeriya.

A cewar rahoton da majalaisar ta fitar kan karancin abinci a duniya ta ce a duniya ta yi fama da karancin abinci wanda aka yi kiyasin cewa ya shafi mutane miliyan dari da goma sha uku.

Rahoton wanda aka sanar jiya a birnin Brussels din kasar Belgium ya ce rikice-rikice da kuma matsalar sauyin yanayi na daga cikin dalilan da suka ta’azzara matsalar ta karancin abinci.

Haka zalika majalisar dinkin duniya ta ce ba ya ga Najeriya sauran kasashen da suka yi fama da matsalar karancin abincin sun hada da: Afghanistan da jamhuriyar Dimukuradiyar Congo da Ethiopia da Sudan ta kudu da Sudan da Syria da kuma Yemen.

Rahoton na majalisar dinkin duniya ya kuma ce matsalar ta fi kamari a kasashen Yemen da jamhuriyar dimukuradiyar Congo da Afghanistan da Ethiopia da kuma kasar Syria.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *