Kotu ta bada umarnin cigaba da tattara sakamakon Zabe a Bauchi

A Najeriya wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta baiwa hukumar zaben ta kasar INEC damar cigaba tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi.

Da yake yanke hukunci alkalin kotun mai shar’a Inyang Ekwo ya yi watsi da hukunci da ya bayar tun da farko na dakatar da tattara sakamakon.

Bayan jin bayanan da suka kamata ne kuma a yau litinin alkalin kotun ya baiwa hukumar INEC damar ci gaba ayyukan ta kamar yadda doka ta bata dama.

Jam’iyyar APC ce dai ta shigar da kara gaban kotun tana kalubalantar hukumar ta INEC da ta dakatar da karbar sakamakon karamar hukumar Tafawa Balewa bisa zargin tafka magudi.

Jam’iyyar dai ta shigar da karar ne tana kalubalantar hukumar ta INEC bisa ikirarin da ta yin a ci gaba da karbar sakamakon karamar hukumar bayan an ayyana zaben jihar a matsayin wanda bai kammala ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *