Kotun sauraran korafin zaben shugaban kasa, ta ki amincewa da bukatar da dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da jam’iyyar sa ta PDP, su ka gabatar na neman kotun da ta tursasa Hukumar INEC basu damar nazartar rumbun adana bayanan ta wato server, wadda ta yi amfanin da shi a zaben shugaban kasa, na ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kotun mai kunshe da alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari’a Muhammed Garba da gagarumin rinjaye, ta ki amincewa da bukatar jam’iyyar PDP da d’an takararta Atiku Abubakar, tana mai cewar, amincewa da hakan, daidai ya ke da gabatar da hukunci kafin kammala shari’a.

Kotun dai ta amince da bukatun wadanda aka gurfanar wato Hukumar zabe ta kasa (INEC) da shugaba Buhari da kuma jam’iyyar APC.

Mai shari’a Muhammed Garba ya kuma ce, tun farko dama Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta ce ba ta yi amfani da rumbun adana bayanai ba wato Server, a don haka ba daidai bane kuma a ce kotun ta umarci Hukumar zabe ta kasa (INEC) da ta bai wa jam’iyyar PDP da d’an takarar ta Atiku Abubakar damar duba rumbun adana bayanai na Hukumar.

Kotun ta kara da cewa amincewa da bukatar PDP da Atiku Abubakar ya nuna karara cewa, ta gamsu kuma ta tabbatar da cewa Hukumar zabe ta kasa INEC ta yi amfani da rumbunan adana bayananta wato server wajen karbar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar ashirin da uku ga watan Fabrairu.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *