Kungiyar Go Round ta yi nasarar doke Kano Pillars da ci 2-1 a wasan mako na bakwai rukuni na biyu a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria da suka fafata.

Go Round ce ta fara cin kwallo ta kafar Akaba Otega a minti na 33 da fara wasa, sai dai daf da za a je hutu Pillars ta farke ta hannun Rabiu Ali.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Go Round ta kara cin kwallo na biyu ta hannun Adeseun Adelani, wanda hakan ya ba ta damar hada maki uku a fafatawar.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga: Rivers Utd 0-0 Kwara Utd da Remo Stars 0-1 MFM da Kada City 2-1 El-Kanemi da Abia Warriors 1-0 Heartland da kuma FC Ifeanyiubah 2-0 Gombe Utd

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *