Kungiyoyin kwadago sun baiwa gwamnatin Najeriya wa’adi

Gamayyar kungiyoyin kwadago a Najeriya sun baiwa gwamnatin kasar wa’adin kwanaki ashirin da daya game da batun sabon tsarin mafi karancin albashi wanda aka tsara tun da fari za a fara biya a watan Satumba.

A yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a garin Ibadan babban birnin jihar Oyo, kungiyoyin sun yi Allawadai da kalaman da ministan kwadago Dr. Chris Ngige ya yi na cewa; gwamnati ba za ta fara biyan sabon tsarin mafi karancin albashin a watan Satumba kamar yadda ta tsara tun da farko ba.

Sun ce duk wani yunkurin watsi da bukatar ta su cikin wa’adin kwanaki ashirin da daya zai sanya ma’aikatan, su ga basu da wani zabi da ya wuce su tsunduma yajin aiki.

Shugaban gamayyar kungiyoyin ma’aikatan Kwamared Andrew Emelieze, ya ce; rashin cika alkawarin fara biyan mafi karancin albashin a watan Satumba zai sa ma’aikatan kasar nan su yanke kauna ga wannan gwamnati.

Kwamared Andrew Emelieze, ya kuma ce; sun gamsu kwarai da bukatar da uwar kungiyar kwadago ta kasa NLC da takwararta ta manyan ma’aikata TUC su ka gabatarwa gwamnati na neman amincewa da kaso daya cikin dari na albashin shugaban kasa  ya kasance a matsayin mafi karancin albashi yayin da rabin kaso na albashin kuma ya zama mafi karancin kudin fansho.

One comment

Leave a Reply to MUTARI ABDULLAHI YGB Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *