Luca Modric ne ya lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon duniya na 2018

Luca Modric dan wasan Croatia da Real Madrid, ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na 2018, wadda ake yiwa lakabi da Ballon d’Or.

Modric shine ya lashe kyautar dan wasan da babu kamarsa a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018, wadda Faransa ta lashe.

Haka kuma shine wanda aka zaba a matakin dan kwallon da ya fi yin fice a nahiyar Turai a shekarar nan. Dan kwallon Portugal da Juventus, Cristiano Ronaldo ne zakaran 2017, kuma yana cikin ‘yan takara har da Lionel Messi na Barcelona

‘Yar wasan tawagar kwallon kafar Norway, Ada Hegerberg ce ta lashe kyautar Ballon d’Or ta mata a karon farko da aka sa mata a cikin bikin karramawar.

‘Yar wasan mai taka leda a Lyon mai shekara 23, ta ci kofin Zakarun Turai uku da na gasar kwallon Faransa hudu da na kalubalen Faransa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *