Majalisar Jigawa tayi gyara kan dokokin shari’a

Majalisar dokokin Jihar Jigawa ta amince da dokar gudanar da shariar manyan laifuka, wadda ta kunshi gyare gyare kan yadda ake gudanar da sharia a Jihar.

A sabon gyaran da akayi, babu wata kotu ko hukuma da zata kama dangin mai laifi a madadin wanda ya aikata laifi.

Mataimakin shugaban masu rinjaye kuma wakilin mazabar kazaure, Barrister Bala Hamza Gada shine ya karanta rahoton da majalisar ta amince dashi.

Shugaban majalisar Hon. Idris Garba Kareka ya amince da yin karatu na uku bayan karbar rahoton kwamatin.

Source: JSHA/page

Two comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *