Masu garkuwa sun saki Malam Ahmad a Najeriya

An sako fitaccen makarancin Alkur’anin nan a Najeriya Sheikh Ahmad Suleiman, wanda wasu ‘yan bindiga su ka sace shi da abokan tafiyar sa a kwanakin baya.

A yayin zantawa da gidan rediyo freedom ta wayar tarho wani makusancin Shehin Malamin, Alaramma Isma’il Maiduguri ya ce an sako Sheikh Ahmad Suleiman kuma yana cikin koshin lafiya.

A cewar sa, Shehin Malamin tare da abokan tafiyar sa suna kan hanyar su ta zuwa Kano daga inda ‘yan bindigar suka boye su.

Rahotanni sun ce, wasu ‘yan bindiga ne suka sace Sheikh Ahmad Suleiman tare da wasu mutane biyar, kwanaki goma sha uku da suka gabata akan titin da ya hada garuruwan Sheme da Kankara a jihar Katsina.

Shi dai Sheikh Ahmad Suleiman da sauran mutanen biyar suna kan hanyar su ta zuwa Kano daga birnin Kebbi babban birnin jihar Kebbi lokacin da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *