Murar tsintsaye tayi sanidiyar mutuwar dubban Kaji a Najeriya

Sama da kaji dubu uku da dari tara ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar murarar tsuntsaye wadda ta bula a jihar filato a baya-bayan nan.

Babban jami’in asibitin kula da dabbobi ta kasa da ke jihar filato Dr. Spak Shaset ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a garin Jos.

Ya ce annobar murar tsuntsayen ta shafi wasu manyan gidajen gona guda biyu a garin Jos.

Haka kuma ya ce, ko a watan Janairun da ta gabata ma an samu irin wannan annobar murar tsuntsayen a  wasu sassa na jihar Bauchi.

Dr. Spak Shaset, ya ce bayan sun dauki samfarin kwayar cutar a matakin gwaji sun tababatar da cewa cutar murar tsuntsaye ce, kuma kawo yanzu tuni suka dauki matakin gaggawa domin dakile cutar don gudun kamuwar wasu gidajen gona a yankin.

Haka zalika ya shawarci masu kiwon dabbobi a jihar ta Filato da su kula da dabbobinsu ta hanyar basu kulawar da ta kamata tare da kai rahoton irin wannan cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *