Najeriya na da wahalar gudanar da kasuwanci – Bankin Duniya

Najeriya ta sauko matsayi na 146 daga matsayin da ta ke na 145 a shekarar da ta wuce (2017), a jerin kasashen duniya da aka fi saukin gudanar da kasuwanci.

Rahoton da bankin duniya ke fitarwa a duk shekara wanda aka fitar a jiya Laraba, ya ce, an yi amfani da manufofi da gwamnatocin kasashe ke fitarwa har guda 314 a kasashe 128 wajen fitar da sakamakon rahoton.

Da ya ke Karin haske kan batun shugaban bankin duniya, Jim Yong Kim, ya ce, wajibi ne gwamnatoci su bullo da sabbin tsare-tsare da za su saukaka harkokin kasuwanci a kasashen su.

Haka kuma rahoton na bankin duniya ya kuma ce a yankin kasashen afurka da ke kudu da hamadas-Sahara an gudanar da sauye-sauye guda dari da bakwai, lamarin da bankin na duniya ke cewa abin a yaba ne.

A cikin rahoton na bankin na duniya, ya kuma ce, Najeriya ta gudanar da sauye-sauye guda hudu, ciki har da wani shirin fara kasuwanci a saukake a jihohiin Kano da Lagos.

Sai dai a cewar shugaban bankin na duniya, Jim Yong Kim, akwai bukatar kara kokari wajen gudanar da sauye-sauye da za su saukaka hanyoyin kasuwanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *