Najeriya ta samu gurbin gasar cin kofin nahiyar Afrika na 2019

Najeriya ta samu gurbin gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Kamaru a 2019 bayan ‘yan wasan Super Eagles sun yi kunnen-doki da takwarorinsu na Bafana-Bafana da ci 1-1.

Wasan da aka doka a  Afirka ta Kudu, Najeriya ce ta soma zura kwallo lokacin da dan wasan Afirka ta kudu Buhle Mkhwanazi ya so kade kwallon da takwaransa na Najeriya Samuel Kalu ya buga amma ta fada ragarsu, minti goma da soma wasa.

Afirka ta kudu ta samu damar cin kwallo a minti na 18 bayan dan wasanta Thamsanqa Mkhize ya mika wa takwaransa Lebo Mothiba tamaula amma ya kasa kammala aikin.

A minti na 26 ne Percy Tau ya keta ‘yan wasan bayan Najeriya inda ya mika wa takwaransa Mothiba kwallon da bai yi jinkiri ba wajen zura ta aka tashi 1-1.

 

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *