Rasha na adawa da takunkumi a kan Siriya

A wannan Talatar ce kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya ke shirin kada kuri’ar amincewa da kudurin kakaba wa gwamnatin Siriya takunkumi, saboda amfani da makamai masu guba. Sai Rasha za ta hau kujerar naki.

Faransa da Amirka da Birtaniya ne dai suka gabatar da kudurin, bayan gudanar da karin bincike kan zargin amfani da makamai masu guban a kan ‘yan tawaye a bangaren Siriyar.

Sai dai tuni Rasha ta nuna manufarta na hana cimma aiwatar da kudirin ta hanyar hawa kujerar naki. Rashan dai ta kasance mai goyon baya tare da tallafawa gwamnatin Siriya tun bayan barkewar yakin kasar da ya ki ci yaki cinyewa.

A baya ta sha zama kadangaren bakin tulu na cimma kakaba wa Damaskus takunkumi a kwamitin sulhun, saboda matsayinta na mai zaunanniyar kujera.

Sauran kasashen da ke da wannan kujera sun hadar da Amirka da Faransa da Birtaniya, wadanda su ne ke goyon bayan ‘yan tawayen Siriyar da ke fada da gwamnati. Kuma dole ne dukkansu su amince kafin zartar da kowane kudiri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *