Rohr zai raba gari da Super Eagles

Wasu rahotanni na nuni da cewa kociyan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Gernot Rohr na gab da ajje aikinsa inda zai koma horar da kungiyar kwallon kafar Aljeriya.

Gernot Rohr wanda ya tsawaita kwantiraginsa da Najeriya zuwa 2020 gabanin tafiya gasar cin kofin duniya, ya ce babu tabbacin dorewar aikinsa bayan rashin nasarar Super Eagles a Rasha.

Kociyan wanda ya dade yana aikin horar da kasashen Afrika irinsu Nijar Birkinafaso da kuma Gabon zai iya tafiyar da tawagar ta Algeria la’akari da cewa ya horar da kungiyoyi kamar su Bordeaux OGC da Nice da kuma Nantes na Faransa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *