Russia 2018: Najeriya ta fitar da ‘Yan wasanta

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta fitar da sunayen ‘yan wasan da za su wakilci kasar a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha cikin watan Yuni.

Cikin ‘yan wasan dai akwai masu tsaron gida wadanda suka hada da Ikechukwu Ezenwa da ke Eyimba International (Najeriya) da Daniel Akpeyi dake Chippa United (Afrika ta Kudu) da kuma Francis Uzoho dake Deportivo de La Coruna (Spaniya).

Masu tsaron baya

William Ekong dake Busaspor (Turkiyya) da Leon Balogun dake Brighton Hove Albion (Ingila) da Kenneth Omeruo dake Kassimpasa (Turkiyya) da Bryan Idowu dake FC Amkar Perm (Rasha) da Chidozie Awaziem dake FC Nantes (Faransa) da Shehu Abdullahi dake Busaspor (Turkiyya) da Elderson Echiejile dake Cercle Brugge K.S.V. (Belgium) da kuma Tyronne Ebuehi dake Benfica (Portugal).

‘Yan wasan tsakiya

Mikel John Obi dake Tianjin TEDA (China) da Ogenyi Onazi dake Trabzonspor (Turkiyya) da John Ogu dake Hapoel Be’er Sheva (Isra’ila) da Wilfred Ndidi dake Leicester City (Ingila) da Oghenekaro Etebo dake UD Las Palmas (Spaniya) da kuma Joel Obi dake Torino (Italiya).

‘Yan wasan gaba

Ahmed Musa dake CSKA Moscow (Rasha) da Odion Ighalo dake Changchun Yatai (China) da Victor Moses dake Chellsea (Ingila) da Alex Iwobi dake Arsenal (Ingila) da Kelechi Iheanacho dake Leicester City (Ingila) da kuma Simeon Nwankwo dake Crotone (Italiya).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *