Sabon kudirin dokar aikin Jarida a Najeriya

Kungiyar masu ruwa da tsaki kan harkokin yada labarai ta Najeriya NPO tare da hadin gwiwar hukumar kula da gidajen Rediyo da Talabijin ta kasar BON sun nuna rashin amincewarsu da sabon kudurin dokar aikin Jarida, wanda suka ce ya saba da kundin tsarin mulkin kasar.

Kungiyar ta NPO dai ta kunshi kingiyar masu gidajen Jarida da kungiyar Editoci ta kasa da kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa NUJ wadanda suka saludanar da wata ganawa a tsakaninsu don fitar da wannan matsaya.

Yayin ganawar ta su sun gano cewa dokar za ta zamo karan tsaye ga ‘yancin fadar albarkacin baki da ‘yancin aikin Jarida tare da kare lafiyarsu, da kuma ‘yancin kafafen yada labarai a kasar.

Kungiyar ta NPO ta kara da cewa yanzu haka batun yana gaban Kotun Kolin Najeriya, kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sa-hannun shugabanta Nduka Obaigbena ta bayyana, gami da sauran takwarorinsa da suka halarci taron.

Sauran wadanda suka sanya hannun su ne shugabar kungiyar Editoci ta kasa Funke Egbemode shugaban kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa NUJ Waheed Odusile da kuma shugaban masu gidajen Rediyo da Talabijin John Momoh.

Sannan kuma sun shawarci Majalisar Dattijai ta jingine batun har zuwa lokacin da Kotun Kolin kasar za tayi hukunci kan makamancin batun da ke gabanta.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *