Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da fara aiwatar da bayar da naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi, ga ma’aikatan kasar na tarayyar da ke karbar kasa da hakan a yanzu.

Shugaban Hukumar Tsara Albashi ta kasar Cif Richard Egbule ya sanar da haka yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce ofishin babban akantan kasar zai duba ya ga lokacin fara aiwatarwar, wanda kuma za a fara biyan ne tun daga lokacin da Shugaban kasar ya sanya hannu a kan yarjejeniyar biyan.

A watan Nuwamban 2018 ne Shugaba Buhari ya bayyana cewa zai aikawa majalisar dokoki kudirin dokar kara albashin, kuma a watan Janairun 2019 majalisar wakilan kasar ta amince da naira 27,000 a matsayin mafi karancin albashi sannan da majalisar dattawa ta amince da naira 30,000 a watan Maris din 2019.

Cif Egbule ya bayyana cewa amincewar ta fara ne daga ranar 18 ga watan Afrilu, kuma za ta shafi albashin hukumomin gwamnati da ke karkashin tsarin albashi biyar.

Sai dai Kungiyar Kwadago ta kasa ta ce za ta gudanar da yajin aiki idan gwamnati ta ki cika alkawarinta kamar yadda ya kamata a kan mafi karancin albashin.

Join the Conversation

2 Comments

    1. Kuma inawa shugaban mu muh’d Buhari Allahu subhanahu wata’ala yasa yagama da duniya lafiya.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *