Shugaba Buhari ya gana da Bola Tinubu a Abuja

Shugaban Najeriya Muhammadu Buharin ya yi ganawar sirri da jagoran jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu a birnin tarayya Abuja.

Sai dai kawo kammala ganawar sirrin ba’a bayyana wa manema labarai mainene makasudun ganawar ta su ba.

Amma kuma ana hasashen cewar ganawar ba zata rasa nasaba da shiga tsakani da shugaban kasa Muhamamdu Bauhari yayi kan rikicin da ‘ya’yan jam’iyyar ta APC suka fada tun bayan kammala zaben fidda gwani a sassan kasar ba.

Rahotanni sun bayyana cewar, ganawar ta su ta dauki lokaci, kuma ya zo dai-dai da kasa da awanni 24 da shugaban yayi liyafar cin abincin dare da ‘yan takarar da aka batawa a yayin zaben na fidda gwani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *