Shugaba Buhari ya yiwa Obasanjo shagube

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo shagube cewa  shi yana neman zango na 2 ne kawai ba zango na 3 ba.

Rahotannin sun bayyana cewar,Tsohon shugaban kasar ya so ya nemi zango na 3 a yayin da yake mulkin kasar a shekara ta 2017, wand ake kira da Third Term Agenda.

Amma kuma majalisar dokoki na kasar nan sun yi watsi da kudirin na tsohon shugaban kasar wanda ya nema a yayin yiwa kudin tsarin mulkin kasar nan kwaskwarima bayan da ya dage akan batun.

Da yake jawabi a dandalin MKO Abiola dake Akure na jihar Ondo  a yayin gangamin yakin neman zaben kan sake zaben shugaban kasa karo na 2, Muhammadu Buhari sai dai bai ambato sunan tsohon shugaban kasar ba, sai dai yace ni ba zango na 3 nake nema ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *