Super Eagles ta doke Seychelles

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta yi galaba a kan ta Seychelles da ci 3-1 a wasan neman gurbin buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a bana.

Najeriya ce ta fara cin kwallo ta hannun Odion Ighalo a bugun fenatiti, sai dai kan aje hutu ne Seychelles ta farke ta hannun Roddy Melanie. Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Super Eagles ta kara guda biyu a raga ta hannun Henry Onyekuru da kuma Moses Simon a karawar da suka yi a filin Stephen Keshi da ke Asaba, jihar Delta, Nigeria.

Najeriya ce ta ja ragamar rukuni na biyar da maki 13, sai Afirka ta Kudu wadda ta yi wasa biyar da maki tara.

Super Eagles ta yi nasarar cin Seychelles 3-0 a wasan farko da suka fafata ranar 8 ga watan Satumba. Libya wadda ita ma ta yi karawa biyar tana da maki bakwai a mataki na uku, sai Seychelles ta hudu mai maki daya kacal bayan karawa shida da ta yi.

A ranar Lahadi 24 ga watan Maris ne Libya za ta karbi bakuncin Afirka ta Kudu a wasa na biyu da za su kece raini a filin wasa na Stade Taieb Mhiri. Kasar Masar ce za ta karbi bakuncin gasar kofin nahiyar Afirka da za a fara ranar 21 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuni.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *