Walter Onnoghen na cigaba da kalubalantar kotu

Dakataccen babban jojin Najeriya Walter Onnoghen yana kalubalantar rashin cancantar alkalin kotun da’ar ma’aikata Danladi Umar wajen cigaba da shari’ar, da ake masa kan zargin kin bayyana kadarorin da ya mallaka

A jiya ne lauyoyin da suke kare Walter Onnoghen suka nemi  Danladi Umar  da ya janye daga cigaba da gabatar da karara a matsayin sa na alkalin kotun da’ar ma’aikata saboda zargin karbar na goro na Naira miliyan 10 da hukumar EFCC ke yi.

Karar mai dauke da sa hannun Chris Uche mai darajar SAN da Chief Sebastine Hon mai darajar SAN da Okon Efut da Chief Ogwu Onoja mai darajar SAN da Noah Abdul da George Ibrahim.

Lauyoyin sun nemi Daladi Umar da ya janye daga cigaba da gabatar da karar saboda rashin cancatar sa

Dakataccen baban jojin kasar ya bayyana Danladi Umar da cewa bashi da aniyya mai kyau, kuma shi ne mai gabatar da karar kuma shi ne alkali a gefe guda kuma shine mai kare wanda ake gabatar da kara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *