Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun kashe mutane talatin da biyar a jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne a wasu kauyuka uku da ke yankin karamar Hukumar Shinkafi.

Wasu mazauna kauyukan sun shaidawa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun iso garuruwan nasu ne akan akan Babura idan suka bude wuta kan mai uwa da wabi ga wasu manoma a kauyen Kwallido da Tungar Kahau da kuma Gidan Wawa.

A cewar su, ‘yan bindigar sun kuma rika bin manoman a guje suna harbin su da bindiga, wanda sakamakon haka daa dama daga cikin su, suka mutu.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *