‘Yan fashi ne suka sace kudin ba Gwaggon Biri ba – Malam Umar Yusif

Hukumomi a gidan ajiye dabbobi da ke jihar Kano wato Kano Zoological Garden, sun ce ‘yan fashi da makami ne ake zargin sun sace kudade da ya kai naira miliyan shida da dubu tamanin da biyu a gidan yarin ba Gwaggon BIRI ba kamar yadda aka yi ta yadawa tun da fari.

Shugaban gidan ajiye dabbobin dajin na Kano Malam Umar Yusif ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Malam Yusif yace a ranar lahadi tara ga watan da muke ciki na Yuni ne mai gadin gidan yarin ya sanar da su cewa ‘yan fashi da makami sun kawo hari sun kuma wawushe kayayyaki da dama a sashen tattara haraji da ke gidan.

A cewar sa, a ranar da lamarin ya faru, ya bar gidan sa da misalin karfe shida da rabi na safiya, bayan isar sa ke da wuya, ya tarar da ofishin sa, dana sauran daraktocin da ke gidan a bude.

Malam Umar Yusif ya kuma ce nan take ba tare da bata lokacin ba ya kira babban jami’in ‘dan sanda ma kula da shiyyar Sharada don sanar da shi halin da ake ciki.

Shugaban gidan ajiye dabbobin ya ce babu kanshin gaskiya cikin rade-radin cewa gwaggon biri ne ya hadiye kudaden, kuma gaskiyar lamari kudaden naira miliyan shida ne da miliyan casa’in ba miliyan shida da tamainin da biyu ba kamar yadda aka yada tun da fari.

Da aka tuntunbi mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna kan faruwar lamarin, ya ce, tuni aka kama mutane goma daga cikin jami’in gidan ajiye dabbobin, ciki har da babban jami’I da ke da hakkin kula da harkokin kudi Lawan Dandadarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *