‘Yan Najeriya sama da 100 sun dawo gida daga Libiya – NEMA

Hukumar bada agajin gaggawa a Najeriya NEMA tace ta karbi akalla mutane 141 ‘yan asalin kasar daga kasar Libya, ciki har da mata 11 masu dauke da juna biyu.

Jirgin da ya dauko su daga Libyan ya sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos, bisa tallafin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Duniya.

A cikinsu akwai mata 71 sai kananan yara mata uku da jarirai mata uku, sai maza 53 da kananan yara maza 6 sai jarirai maza 3.

Da ya ke tarbarsu a filin Jirgi babban jami’in shirye-shirye na hukumar ta NEMA Injiniya Segun Afolayan, ya shawarci mutanen da ka da su bari abinda ya faru da su mara dadi ya yi tasiri a rayuwarsu.

Sannan ya bukace su su kasance masu sanin darajarsu da kuma nuna juriya yayin jimamin abinda ya same su, tare da mara baya ga yunkurin gwamnantin tarayya na kyautata dokokin shige-da-fice.

Tun a bara ne dai hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Duniya take ta fafutukar ganin an dawo da ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Libya zuwa gida Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *