‘Yan Najeriya sunyi farar dabara – Bola Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC a Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce, al’ummar kasar sun yi farar dabara wajen baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari daman zarcewa a karo na biyu ta hanyar sake zaben sa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sa da aka fitar jiya Laraba.

Sanarwar ta ruwaito Tinubu na cewa zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata yana daya daga cikin zabuka mafi nagartar da inganci da aka taba gani a tarihin kasar nan.

A cewar Bola Tinubu al’ummar kasar nan sun ga nagartar shugaba Buhari shi yasa suka sake amincewa da ya zarce a karo na biyu.

Ya kara da cewa yana da kwarin gwiwa shugaba Buhari zai bai wa marada kunya wajen kai kasar nan ga tudun mun tsira.

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *