Yau ce ranar wayar da Kai kan cutar Sikila 2019


Yau ne ake gangamin ranar yaki da cutar Sikila ta duniya. Majalisar dinkin duniya ce ta ware duk ranar 19 ga kowanne watan Yuni domin wayar da kai kan cutar ta Sikila.

Rahotanni sun ce har yanzu ana haifar yara dubbai masu dauke da cutar duk shekara. An yi amanna cewa ba kasafai ake warkewa daga cutar ba, saboda haka ne gwamnatoci da kungiyoyi ke cigaba da wayar da kai kan mahimmancin yin gwaji kafin aure domin kaucewa haifar yara masu dauke da larurar ta Sikila.

Kungiyar masu dauke da cutar Sikila ta jihar Jigawa suma sun bi sahun takwarorinsu na duniya wajen yin wannan gangamin, inda kuma suka bukaci gwamnati ta taimakawa masu cutar da magunguna kasancewar maganin cutar Sikila na da tsada sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *